Wednesday, November 19
Shadow

Kotu ta yankewa dan Tiktok dake saka kayan mata hukuncin daurin shekara 1 a gidan yari

Kotu ta yanke wa ɗan Tiktok mai saka rigar mama da wanka akan titi hukuncin shekara ɗaya a gidan yari.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Kotun Majistiri mai lamba 21 dake zamanta a Gyadi-gyadi, karkashin jagorancin mai sharia Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke wa matashinnan Umar Hashim Tsulange da ya kware wajan sanya rigar mama, yana wanka a titi hukuncin zaman Gidan Gyaran Hali na shekara 1, ko biyan tarar Naira 80,000.

Freedom Radio ta rawaito cewa kotun ta kuma umarci Tsulangen ya biya Hukumar tace Fina-finai Naira 20,000 ladan wahalar da ta yi.

A karshe kotun ta ja hankalin Umar din da ya zama matashi na gari, domin ya kyautata gobensa.

Karanta Wannan  Sojojin Najariya sun ce sun kashe 'yan Bindiga 10,937 da kama guda 12,538 a shekarar 2024

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *