Friday, December 5
Shadow

Lokaci ya ƙure wa Amaechi kan neman takarar shugaban ƙasa – Wike

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya ce lokaci ya ƙure wa tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi kan yunkurinsa na neman takarar shugabancin Najeriya.

Wike wanda ya bayyana haka a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels Politics Today, ya ce ƴan Najeriya ba za su zaɓi Amaechi a zaɓen 2027 ba.

Amaechi wanda yake cikin haɗakar jam’iyyar ADC waɗanda ke yunkurin kalubalantar shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani na kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2022.

Amaechi dai ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC a fafutukar da yake yi na neman kujerar shugaban ƙasa.

Karanta Wannan  An kama dan wasan Real Madrid da yiwa karamar yarinya fyàdè

Sai dai, Wike ya ce Amaechi ba zai samu tikiti a jam’iyyar ADC ba don shiga takara a 2027.

“Amaechi da kansa ya sani cewa ba zai samu tikiti ba. Na ji yana cewa ya san lagon shugaban ƙasa, don haka ya san ta yanda zai kayar da shi. Amma me ya sa ya faɗi a zaɓen fidda gwani a 2022 tun da ya san lagon shugaban ƙasa?”, in ji Wike.

Wike ya soki Amaechi kan kasa yaƙi da cin hanci da kuma rashin shugabanci nagari, inda ya ce bai mutunta ɓangaren shari’a da kuma doka ba lokacin da yake gwamnan jihar Ribas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *