
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa, Jam’iyyar ADC yaudarar talakawa kawai suke ko sun samu mulki babu wani ci gaba da zasu iya kawowa.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV ranar Juma’a.
Datti na wannan maganar ne duk da cewa, Peter Obi wanda suka yi takara tare a yanzu yana jam’iyyar ADC.
Datti dai yace, yana fatan Peter Obi zai koma jam’iyyar Labour party yayi takara acan.
Da aka tambayeshi ko zai sake yiwa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa? Datti Baba Ahmad ya ce Eh.