Yawan fitsari ga mace me ciki ba matsala bane, alamace ta daukar ciki saidai idan yayi yawa, yakan iya zama cuta.
Yawan fitsari na faruwa ne ga mace me ciki saboda yanda jikinta yake canjawa saboda shigar ciki da kuma shirin haihuwa.
Yawan fitsari na daga cikin alamun farko na daukar ciki.
Yawanci yawan fitsari na farawane a mako na 10 zuwa 13 bayan mace ta dauki ciki.
Yawanci mata masu ciki kan yi fitsari sau 6 zuwa 10 a rana. Saidai idan ya wuce haka, yana iya zama na ciwo.
Kalan fisarin mace me ciki yakan kara duhu, daga ruwan dorawa, watau Yellow zuwa me ruwan dorawa sosai ko kuma Dark Yellow.
Idan mace me ciki ta ji fitsari, yana da kyau, kada ta rikeshi, ta je ta yi, saboda rike fitsari yana da illa ga mace me ciki da danta.