Friday, December 5
Shadow

Najeriya ta ƙara kuɗin yin fasfo

Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da ƙarin farashin yin fasafo wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025, domin inganta inganci da tsaro a tsarin fasafo ɗin ƙasar.

A cewar hukumar, farashin fasafo na shekaru biyar mai shafi 32 wanda a baya yake kan naira 70,000 yanzu zai tashi zuwa naira 100,000, yayin da na shekaru 10 mai shafi 64 wanda a baya yake kan naira 120,000 zai koma naira 200,000.

Sai dai, farashin fasafo da ‘yan Najeriya ke yi a ƙasashen waje ba zai canza ba, inda za a ci gaba da biyan dala 150 kan fasafo na shekara 5 da dala 230 kan fasafo na shekara 10.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Sadiya Haruna ta fito ta kare Samha M. Inuwa kan zargin Bidiyon Tsyràìchy tace karyane Samha bata zuwa Abuja tana rabawa kuma bata Video call da maza

Hukumar ta bayyana cewa wannan sabon tsarin na nufin tabbatar da daidaito a ayyukan fasafo, tare da sauƙaƙa damar samun fasafo ga duk ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *