
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ba zai iya kayar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe ba a 2027.
Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ce ta bayyana hakan ta bakin me magana da yawunta, Mr Seye Oladejo inda yace an wuce da irin siyasar da Goodluck Jonathan ya saba da ita
Yace a tarihi idan aka tuna, Goodluck Jonathan ya bar Najeriya da matsaloli da yawa
A shekarar 2015 ne dai Goodluck Jonathan ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.