
A jiya ne dai rahotanni suka bayyana cewa, An kaiwa taron jam’iyyar ADC hari a Kaduna inda aka lalata dukiyoyi.
Taron wanda tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya jagoranta ya dauki hankula sosai.
Daga baya, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya fito inda yake bayyana zargin Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da daukar nauyin wadanan ‘yan daban.