
A’isha Abubakar wadda ta fito daga jihar Nasarawa ta shiga gasar Sarauniyar kyau ta Najeriya.
Saidai abinda yafi daukar hankali game da ita shine shigarta inda ake ganin ta da kaya masu nuna surar jiki wadanda basu dace da addini da al’adar Mutanen Arewa ba.
Da yawa dai sun soke ta game da hakan inda a wasu lokutan takan mayar da martani.
Saidai an yi an gama gasar kuma wadda ta fito daga jihar Anambra ce ta lashe gasar.
Hakan yasa da yawa suke wa A’isha Allah kara da fadar cewa, duk da nuna tsiraicin da ta yi amma gashinan bata ci gasar ba.
A’isha dai tace har yanzu ita daliba ce sannan kuma tana sana’ar tallar kayan sakawa.