
Matar tauraron mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara watau, Hajiya Aishatulhumaira ta jawo cece-kuce bayan wallafa wakar yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da ta yi.
Ta yi wakar ne tare da wani me suna Hafiz Abdallah inda ta nemi mutane su je shafinta na YouTube su kallah.
Saidai yayin da wasu suka yaba, wasu kuwa sun bayyana cewa hakan bai dace ba.
A baya dai an ga yanda Rarara da A’ishatulhumaira suke waka tare.