
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi ikirarin cewa a lokacin da ya hau mulki a watan Mayu na shekarar 2023 ana sayen dalar Amurka ne akan Naira 1,900.
Saidai da yawa sun ce wannan ikirari na shugaban kasa ba gaskiya bane.
Daya daga cikin wanda suka karyata maganar shugaban kasar, Akwai Rufai Oseni me gabatar da shirye-shirye na tashar Arise TV inda yace wannan magana ba gaskiya bane.
Yace dala ta tashine saboda tsare-tsaren tattalin arziki na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.