Friday, December 5
Shadow

Kungiyar Likitocin Najeriya sun baiwa Gwamnatin tarayya awa 24 ta biya musu bukatunsu

Kungiyar Likitocin NARD tace ta baiwa Gwamnatin tarayya awanni 24 ta biya mata bukatunta.

Hakan na zuwane bayan da kungiyar ta baiwa gwamnatin kwanaki 10 wanda suka kare a ranar 10 ga watan Satumba.

Kungiyar ta bayyana hakane bayan zaman taron da ta yi na tsawon awanni 6 ranar Laraba.

Shugaban kungiyar, Dr. Tope Osundara ya tabbatar da hakan inda yace suna sane da alkawarin biya musu bukatunsu da gwamnati ta yi amma suna son gani a kasa.

Kungiyar tace idan a karshen ranar Alhamis basu ga hakkokinsu da suke bi ba, ranar Juma’a zasu tashi da yajin aiki.

Karanta Wannan  Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu kuɗin gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Aba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *