
Jihar Delta ta yi sabuwar doka game da irin kayan da ya kamata ma’aikatan jihar maza da mata su rika sakawa.
A wata sanarwa data fitar a yau, Alhamis, Jihar tace dolene ma’aikata su rika saka kayan mutunci a yayin da suka je wajan aiki.
Sanarwar tace ana tsammanin maza su rika saka kwat ko riga ‘yar ciki su tsuke in banda ranar Juma’a da zasu iya saka kayan gida.
Hakanan ba’a so mutum ya tara gemu da yawa ba aski, ba gyara.
Mata kuma su saka siket wanda zai rika wuce gwiwarsu.