
Rahotanni sun bayyana cewa, Labarin dake yawo cewa, tsohuwar matar Ahmad XM, Watau Safiya zata auri Hambali ba gaskiya bane.
Safiyar da kanta ta fito ta musanta wannan labari inda kuma wasu na kusa da ita suma duk suka karyata wannan labari.
Bayan rabuwarta da tsohon mijinta, Ahmad XM, An yada labaran cewa zata sake aure inda zata auri Hambali, kuma da dama sun zata hakan gaskiyane.
Saidai daga baya labari ya bayyana cewa, ba gaskiya bane wannan ikirarin.