
‘Yan kasuwar man fetur sun koka da cewa, Dangote na sayarwa da kasashen waje man fetur a farashi me sauki fiye ye da yanda yake sayarwa a Najeriya.
”Yan kasuwar sun ce ‘yan kasar waje na samun ragin kusan Naira 65 akan kowace Lita idan aka kwatanta da farashin man da Dangoten ke sayarwa a Najeriya.
Dan hakane ma suka ce wani lokacin basa saye a wajan Dangote sai su je wajan ‘yan kasar wajen da ya sayarwa su saya a hannunsu su shigo dashi Najeriya.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar DAPPMAN, Olufemi Adewole ne ya bayyana haka ga manema labarai na Punchng.
Yace abinda suke nema a wajan Dangote shine ya rika musu sauki dan haka sai su daina shigo da man daga kasashen waje suna saye a hannunshi.
Yace Dangote da gangan yake karya farashin mai da zarar ya ga sun kawo mai daga gasashen waje.