Friday, December 5
Shadow

Wallahi Karya nake, kawai ina neman followers ne dan in samu kudin abinci, ina zan kai masa 100>>Inji Mandy Wadda tace zata yi Alfasha da maza 100 saboda ta shiga kundin Tarihin Duniya

Ayomiposi Oluwadahunsi wadda tace zata yi lalata da maza 100 dan ta samu shiga kundin tarihin Duniya a jihar Legas a yanzu tace da wasa take.

Ta bayyana hakane bayan da basaraken Ogun Oba Akintunde Akinyemi yayi kira da a kamata a mata gwajin kwaya sannan a kaita gidan mahaukata.

Tace ta yi hakanne kawai dan ta samu mabiya dan kuma ta samu ana bata tallata amma ba zata iya yin lalata da maza 100 ba.

Karanta Wannan  Ganin Hoton El-Rufai da Peter Obi ya dauki hankula sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *