
Malamin Addinin Musulunci, Dan Darika, Dr. Murtala Abubakar Argungun ya bayyana cewa, shi a wajensa babu Musulmi makiyin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Malam yace ko da wadanda basa Maulidi baya daukarsu a matsayin makiyan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) kawai dai akwai sabanin fahimta ne kan yanda ya kamata a girmama Annabi.
Wannan kalamai nasa sun jawo masa yabo sosai inda mutane ke cewa haka ya kamata a rika wa’azi.