Friday, December 5
Shadow

Darajar naira na farfaɗowa

Farashin dalar Amurka na ci gaba da sauka a Najeriya, inda a wasu kasuwannin bayan fage ake sayar da dalar daya a kusan naira 1,450.

Wannan farashi ya yi kasa idan aka kwatanta da na makonnin baya, inda darajar dala ta kai har naira 1,560 a wasu wuraren.

A jihar Kano, cibiyar harkokin kasuwancin arewacin Najeriya, masu hada-hadar kudaden kasashen ketare sun tabbatar da cewa farashin dalar na ta sauka a kullum.

Shugaban ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen waje a jihar, Alhaji Sani Salisu Dada, ya ce, “Dangane da faduwar darajar dala, kusan sati biyu kenan a kowace rana tana karyewa. Idan aka duba baya, dalar ta kai kusan naira 1,560, amma a yau Babban Bankin ƙasa yana sayarwa a kan naira 1,466, yayin da kasuwar bayan fage take a naira 1,450.”

Karanta Wannan  Fastar yakin neman zaben Gwamnan jihar Gombe ta Sheikh Pantami ta bayyana

“A halin yanzu farashinmu ya fi armashi, saboda yana kusa da na CBN,” in ji shi.

A cewar Dr Abdulrazak Fagge, masanin kimiyyar kasuwanci a Najeriya, akwai yiwuwar naira ta ƙara daraja kan dala a cikin makon da ke tafe.

“Daga nan zuwa mako mai zuwa, naira za ta dinga samun tagomashi a kan dala,saboda idan aka lura, dalar na sauka ne a duk fadin duniya, ba a Najeriya kaɗai ba tun bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya kafa haraji kan wasu kasashe, abin da ya haifar da martani daga wadannan kasashe.” in ji shi.

Rahotanni sun nuna cewa akwai wasu dalilai da suka taimaka wajen rage darajar dalar a Najeriya, ciki har da sabon tsarin da wasu bankuna suka kirkiro na bai wa matafiya damar samun katin ATM mai ɗauke da dala dubu hudu.

Karanta Wannan  Karya ake mana bamu biya Biliyan 6 ba na diyyar mafarautan Kano da aka kònà>>Inji Gwamnatin jihar Edo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *