
Tsohon shugaban Hukumar kididdiga ta kasa, NBS, Yemi Kale ya bayyana cewa, Najeriya ce ta biyu bayan India da ta fi kowace lasa yawan matalauta.
Yace akwai matalauta Miliyan 89 a Najeriya wanda hakan yana nufin kaso 40 na ‘yan Najeriya matalauta ne.
Ya bayyana hakane a cikin sakoshi na ranar ‘yanci.
Yace babban abinda ke kawo Talauci shine yanda gwamnati bata yin tsare-tsare masu kyau.