
Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana jin dadinsa game da matakan da babban bankin Najeriya CBN ya dauka wajan magance yawan kudi a hannun mutane.
Sarki Sanusi yace hakan yasa hauhawar farashin kayan abinci ya ragu duk da dai har yanzu yana kan maki 20 wanda yayi yawa.
Sarkin yace tattalin arzikin Najeriya ya dawo daga hanyar rugujewa da ya dauka saboda wanan mataki da CBN ya daka.