Friday, December 5
Shadow

Nima ina goyon bayan a saki Nnamdi Kanu>>Inji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, yana kira a saki shugaban Kungiyar ‘yan Ta’addha ta ÌPÒB dake son kafa kasar Biafra, watau Nnamdi Kanu.

Atiku yace ci gaba da rike Nnamdi Kanu kamar budadden ciwo ne ga ‘yan Najeriya dake ci gaba da yiwa mutane zafi.

Sannan kuma sabawa doka ne.

Yace kin bin umarnin kotu data bayar da belinsa kama karyane da kuma take hakki.

Atiku yace dan haka yana goyon bayan Zanga-zangar da Sowore ya shirya ta neman a saki Nnamdi Kanu.

Yace Najeriya ta gaza idan aka ci gaba da kyale Nnamdi Kanu a tsare

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Gobara ta tashi a wajen sayar da Gas a Rijiyar Zaki Kano, Ji yanda Tukwanen Gas suka rika fashewa suna kara kamar Bàm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *