
Majalisar kasar Peru ta tsige shugabar kasar me suna Dina Boluarte saboda yawaitar kisa a kasar.
Rahotanni sun ce majalisar ta gayyaci shugabar kasar da ta gurfana a gabanta amma ta ki amsa gayyatar da aka mata.
Dalili kenan ranar 10 ga watan Oktoba aka tsigeta.
Yawan mutanen da aka kashe a kasar tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar watan Augusta sun kai mutane 6000.
Duka ‘yan majalisar 124 sun amince da tsige shugabar kasar ba tare da ko guda daya yace bai yadda ba.
Shugaba Dina Boluarte ce aka bayyana wadda tafi bakin jini a Duniya.