
Jagoran adawar Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirari samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi.
Cikin wani bidiyo da ya fitar, da tsakar daren da ya gabata, Mista Bakary ya gode wa al’ummar Kamaru kan ”yarda da samar da canji” da ya ce sun yi a ƙasar.
Iƙirarin nasa na zuwa a daidai lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓukan.
“Ina son bayyanawa cikin girmamawa da nutsuwa cewa al’ummar Kamaru sun yi zaɓinsu, don haka ya kamata a martaba zaɓinsu,” in ji Bakary.
Ya kuma alƙawarta wallafa cikakken sakamakon zaɓukan daga rumfunan zaɓen ƙasar.
“Haƙiƙa wannan nasara ba tawa kaɗai ba ce ni kaɗai, ta kowa ce,” in ji shi.
Kawo yanzu hukumomin Kamaru ba su ce komai ba game da iƙirarin jagorar adawar, to amma a baya ministan cikin gida na ƙasar, Paul Atanga Nji ya nanata haramcin iƙirarin nasara daga ɗaiɗaikun ƴantakara tare da wallafa abin da ya kira ”haramtaccen” sakamakon zaɓe.