
Rahotanni sun watsu sosai cewa, Gwamnatin Tarayya ta soke jarabawar JAMB a matsayin ma’unin shiga jami’a.
Saidai a martanin Gwamnatin ta bakin ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa CON, yace wannan labari ba gaskiya bane kuma ba daga hannunsu ya fito ba.
Yace domin kawar da duk wata tantama, JAMB har yanzu itace jarabawar da dalibai zasu rika yi dam samun damar shiga jami’a.
Yace kuma zasu ci gaba da hada kai da JAMB dan cimma burikan Ilimi.