Friday, December 5
Shadow

Hukumar ‘Yansanda ta sanar da dalilin da yasa ta kama Omoyele Sowore

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta sanar da dalilin kama dan fafutuka kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore.

Kakakin ‘yansandan Najeriya, Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an kamashi ne saboda saba umarnin kotu na zuwa zanga-zanga guraren da kotun ta haramta yin hakan.

Ya bayyana cewa, wadanda aka kama saboda zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu din yanzu jimulla su 14 ne.

Yace wadanda suka kama bayan da Sowore ya tsere sun bayyana cewa shine ya jagorancesu zuwa yin zanga-zangar.

Yace dan haka rashin kama Sowore zai zama kamar ba’a yi adalci ba kenan.

Ya kara da cewa ba zai wuce awanni 24 a wajansu ba, zasu gurfanar dashi a gaban kotu dan a yanke masa hukunci, kamar sauran.

Karanta Wannan  Kalli Sabon Bidiyo da Duminsa: Duk da ta kutsa kai cikin Farfajiyar majalisar tarayya da karfin tsiya, An kulle ainahin cikin zauren Majalisar aka hana sanata Natasha Akpoti shiga ciki, yayin da su Akpabio ke ciki, Ji abinda ya kuma yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *