Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Sati daya bayan rahotannin yunkurin jhuyin mulki Shugaba Tinubu ya kori manyan sojoji, Ya sauke Janar Christopher Musa daga shugaban sojoji, ya baiwa Gen. Olufemi Oluyede shugaban sojojin Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron ƙasar, a wani sauyi a tsarin jagorancin sojjin ƙasar domin inganta da ƙarfafa sha’anin tsaro a Najeriya.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar mai sa hannun ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban a harkar watsa labarai, Sunday Dare, Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin.

Jadawalin sabbin hafsoshin:

  • Janar Olufemi Oluyede – Hafsan hafsoshi
  • Manjo Janar W Sha’aibu – Hafsan sojojin ƙasa
  • Air Vice Marshall S.K Aneke – Hafsan sojin sama
  • Rear Admiral I. Abbas – Hafsan sojin ruwa
  • Manjo Janar E.A.P Undiendeye – Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji.
Karanta Wannan  Dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya bayar da tallafin Naira Miliyan 100 ga dalibai a jihar Borno

Waɗanda suka tsira:

  • Mallam Nuhu Ribadu – Babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
  • Kayode Egbetokun – Sifeto Janar na ƴansanda.
  • Manjo Janar EPA Undiandeye – Shugaban sashen tattara bayanan sirri na soji.

Naɗin hafsoshin da Tinubu ya yi a 2023

A watan Yunin 2023 ne shugaba Tinubu ya rushe hafsoshin tsaro da ya gada daga gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari inda kuma ya naɗa sabbin mutanen da suka maye gurbin tuɓaɓɓin.

Jerin sunayen hafsoshin tsaron da aka naɗa a 2023:

  • Mallam Nuhu Ribadu – Babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
  • Manjo Janar Christopher Musa – Hafsan hafsoshi.
  • Manjo T. A Lagbaja – Hafsan sojin ƙasa.
  • Rear Admirral E. A Ogalla – Hafsan sojin ruwa.
  • AVM H.B Abubakar – Hafsan sojin sama.
  • DIG Kayode Egbetokun – Sifeto Janar na ƴansanda
  • Manjo Janar EPA Undiandeye – Shugaban sashen tattara bayanan sirri na soji.
Karanta Wannan  Hotuna: Kasar Libya ta kulle 'yan kwallon Najeriya a filin jirgi ta hanasu zuwa ko ina

Bisa jadawalin tsaffin hafsoshin, za a fahimci cewa tsohon hafsan sojojin sama, Manjo T.A Lagbaja shi ne wanda ya rasu a ranar 4 ga wtaan Nuwamban 2024, inda kuma Janar Olufemi Oluyede ya maye gurbinsa.

A yanzu haka Janar Olufemi Oluyede ya samu ƙarin girma inda ya maye gurbin Manjo Janar Christopher Musa a matsayin Hafsan hafsoshin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *