
Sanata Natasha Akpoti ta bayyana cewa, hukumar kula da shige da fici ta Najeriya, NIS ta kwace mata fasfo dinta inda ta hanata fita kasar waje.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data dauka a filin jirgin inda tace jami’an sun ce mata Sanata Godswill Akpabio ne yasa a kwace mata fasfon wai saboda idan ta fita kasar waje tana zuwa ta yi hira da kafafen yada labarai tana zubarwa da Najeriya mutunci a idon Duniya.
Tace babu wata kotu data bada umarnin a kwace mata fasfon nata.
Ta bayyana hakan da take mata hakkinta kasancewar shekarar ta biyu kenan da zama ‘yar majalisa dan hakane ta ke son zuwa kasar waje dan shakatawa.
Zuwa yanzu dai Sanata Godswill Akpabio ko ma’aikatar NIS basu ce uffan ba kan lamarin.