ANA BIKIN SALLAH YAN BINDIGA SUN TAFKA MUMMUNAN BARNA A SOKOTO.
Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto, inda suka kashe kuma suka sace mutane da dama da sanyin safiyar Lahadi
Maharan sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar, suka kashe mutane sama da goma, kamar yadda aka ruwaito
An ruwaito cewa, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba.
Allah ta’ala yakawo mana zaman lafiya alfarmar Al-qur’ani.