Thursday, July 18
Shadow

Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya lamarin na damunshi.

Ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a wayar da kawunan mutane game da hakan.

Shugaban ya bayyana hakane bayan kammala sallar Idi a jiya, Lahadi.

Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yanda mutane da yawa suka rungumi harkar Noma.

Shugaban yace nasarar kasa ta dogara ne akan zamun shuwagabanni masu nasara akai-akai.

Karanta Wannan  Hotuna: Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Karbi Bakuncin Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai A Gidansa Dake Daura Jihar Katsina, Yau Lahadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *