
Magajin Garin Birnin New York Musulmi na farko ya bayyana cewa, shi musulmi ne kuma yana Alfahari da hakan kuma baya shakkar fadin hakan a gaban koma wanene.
Ya bayyana hakane a jawabinsa na farko tun bayan da ya lashe zaben zama magajin garin Birnin New York City na kasar Amurka.
Hakanan shine Magajin gari mafi karancin shekaru, 34 tun kusan shakaru 100 da suka gabata a birnin na New York City.