
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a karo na 3 ya sake maimaita cewa, ba zai zuba ido yana kallon Irin kokarin karar da kiristoci da ake yi a Najeriya ba.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da shafin Fadar White House ta wallafa.
Trump yace ba lallai ne ‘yan Najeriyar su ji dadin matakin da zai dauka ba amma ba zai zuba ido ba.
Yace bama a Najeriya ba kadai, dama duka Duniya duk inda ake kokarin karar da Kiristoci zasu kai dauki.