
Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wa ƙudirin dokar amfani da ababen hawa masu amfani da lantarki.
Ƙudirin mai taken Electric Vehicle Transition and Green Mobility Bill 2025, Sanata Orji Uzor Kalu (daga jihar Abia) ne ya gabatar da shi, wanda ke neman ɗora Najeriya kan “hanyar kyautata muhalli”.
Mista Kalu ya ce dokar “za ta taimaka wa ɓangaren ƙera ababen hawa, da makamashi, da ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma samar da ayyukan yi”.
“Dokar ta ba da damar yafe haraji, da harajin shigo da kaya, da harajin kan hanya, da bayar da tallafi ga masu amfani da motoci masu amfani da lantarki da masu samar da su,” in ji shi.
Ta kuma tilasta kakkafa tashoshin caji a duka gidajen mai da ke faɗin ƙasar.