
Majalisar Jihar Kano ta mayar da yaren Hausa a matsayin yaren da za’a rika amfani dashi wajan koyar da dalibai a makarantun Firamare da karamar Sakandare.
Majalisar ta aiwatar da wannan doka ne ranar 5 ga watan Nuwamba.
Hakanan Kwamitin majalisar dinkin Duniya na UNESCO ya amince da wannan mataki saboda karfafa Amani da harshen uwa.