
An ga babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi a kasar Turkiyya inda har wakilin kafar yada labarai ta TRTHausa, Bahause ya bayyana cewa sun yi hira da malamin.
Saidai da yawa, Musamman ma ‘yan kudancin Najeriya na cewa ya tsere ne saboda fargabar harin da kasar Amirka tace zata kawo Najeriya.
Saidai babu wasu bayanai dake tabbatar da wannan zargi inda Bahaushe ya mayarwa wani martani bayan ya tambayi yaushe Sheikh Dr. Ahmad Gumi zai dawo Najeriya da cewa, Kwanannan.
Yace masa shine ma zai jagorancin Sallar Juma’a me zuwa in Allah ya yarda.