
Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya haramta amfani da wayar hannu bayan da Bidiyon rikicinsa da wani soja ya bayyana.
A wata sanarwa da aka fitar a ma’aikatar ta kula da babban birnin tarayya Abuja, tace daga ma’aikaci na mataki na 14 zuwa kasa, kada a sake ganin wani ya je wajan aiki da wayarsa.
Sahara Reporters tace lamarin ya kawo rudani a ma’aikatar inda da yawan ma’aikatan hukumar abin ya basu mamaki.
Tuni dai kungiyoyin fafutuka dana kare hakkin bil’adama suka rika Allah wadai da wannan mataki da kuma fadin cewa dakile fadar albarkacin bakine.