
Rahotanni na ta yawo a kafafen sada zumunta cewa, Wai tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya baiwa sojan ruwa da suka kara da Wike, A. Yerima dankareriyar motar Alfarma.
Saidai a sanarwar da ya fitar ta bakin magana da yawunsa, Paul Ibe, Atiku Abubakar yace ba gaskiya bane be baiwa AM. Yerima kyautar mota ba.
Yace labarin karyane kuma yana kira ga mutane su yi watsi dashi.
An dai rika yada cewa Atiku Abubakar ya baiwa sojan ruwan, AM. Yerima kyautar motar Toyota SUV.