
Dan gidan Sarkin Kano, Adam Lamido Sanusi ya kare mahaifinsa, me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II
Yace Bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta dake cewa mahaifinsa na zaune sanda ‘yan mata suka rika rangwada suna nuna kwalliya a wajan Bikin nuna kwalliya da diyarsa ta shirya a Kano ba gaskiya bane.
Yace mahaifinsa, yaje wajenne a lokacin da wasu ke sanye da kaya suna kwaikwayar sarakunan da suka gabata.
Amma baya wajan lokacin da ‘yan mata suka rika rangwada.
A Bidiyon dake ta yawo a kafafen sada zumunta dai an ga mata nata rangwada a wajan inda aka ga wata hadda cire bujenta
Dan sarkin, Adam Sanusi Lamido yace yana ganin nan gaba mahaifin nasu zai daina halartar irin wadannan gurare dan kaucewa yarfe irin wannan