Friday, December 5
Shadow

Matashi dan Fafutuka ya bace a Jigawa biyo bayan wallafa hotunan tallafin da shugaban karamar hukumar Roni ya bayar na Baro da jarkokin dibar ruwa

Wani Matashi me suna Abiyo Roni ya yi batan dabo bayan wallafa hotunan tallafin Baro da jarkokin dibar ruwa da shugaban karamar hukumar Roni ta jihar Jigawa ya baiwa matasa.

Matashin ya saka hotunan ne wanda suka yadu sosai a kafafen sada zumunta suka kuma jawo cece-kuce.

Da yawa sun rika kiran a bayyana inda yace saboda tun bayan wallafa wadannan hotuna aka nemeshi aka rasa.

Ana tunanin dai batan nasa baya rasa nasaba da siyasa saboda yana yawan sukar masu rike da madafan iko.

Karanta Wannan  'Yan Bìndìgà sun yi gàrkùwà da sojojin Najariya 3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *