
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa, jam’iyyar APC kamar Jirgin Annabi Nuhu(AS)take.
Ya bayyana hakane a ranar Asabar wajan karbar wasu sabbin ‘yan siyasa da suka shiga jam’iyyar ta APC.
Yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya basu kudade masu yawa su yiwa mutane aiki shiyasa ma bai ga dalilin da zai hana a sake zaben Shugaba Tinubu a karo na biyu ba.
Yace APC itace jirgin Annabi Nuhu kuma duk wanda bai shiga ba za’a barshi a baya.