
Tsohuwar Firaiministar kasar Canada, Goldie Ghamari ta bayyana cewa, sun gano Najeriya na aiki da kasar Iran a munafurce.
Sannan ta zargi Gwamnatin Tarayya da hannu a matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita da dan jaridar kasar Ingila, Piers Morgan da ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Yusuf Tuggar Maitama.
Tace A tsarin Najeriya ya kamata idan shugaban kasa ya zama musulmi, mataimakinsa ya zama kirista hakanan idan shugaban kasa kiristane, mataimakinsa zai zama Musulmi.
Tace amma a gwamnatin tinubu babu wakilcin kiristoci inda ta zargi cewa ana muzgunawa Kiristoci.