
Sanata Okey Ezea daga jihar Enugu ya rigamu gidan gaskiya.
Sanata Natasha Akpoti da Sanata Orji Uzor Kalu ne suka tabbatar da hakan.
Sanata Kalu a ganawa da manema labarai a Abuja yace ya samu labarin mutuwar Sanata Okey Ezea da gigici inda yace abokin aiki ne kuma dan uwa.
Yace sukan je ma coci tare.