
Ministan Babbban Birnin Tarayya, Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa, doka ta bashi damar kwacewa da baiwa kowa yake so fili.
Ya bayyana hakane yayin ziyarar da shuwagabannin hukumar kula da yankin kudu maso kudu suka kai masa.
Yace idan mutum ya bar filinsa ba tare da ginawa ba na tsawon lokaci, ko kuma ya ki biyan haraji ko ya saba doka zai iya kwace filinsa.
Wike yace baya kwace fili saboda siyasa yace abin takaici ne ace mutane basa son biyan Haraji amma suna son gwamnati ta rika musu aikin gina kasa.