
Shugaban kungiyar ÌPÒB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya rika zagin Alkali a kotu yana cewa bai san shari’a ba.
Kanu yace babu ta yanda za’a yi a yanke mai hukunci da dokar da babu ita a rubuce.
Ya rika maganane yana rike da abin magana watau Lasifika.
Saidai Jami’an DSS sun zagayeshi inda suka rika kokarin Kwace abin maganar daga hannunsa.
Lamarin ya dauki hankula saboda ya ki bayarwa sai da aka yi amfani da karfi.