Eh! Kanunfari yana maganin infection.
Bincike ya tabbatar da cewa, man Kanunfari na dauke da sunadaran Antibacterial, Antifungal, Insecticidal, da kuma Antioxidant.
Dan haka masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, Kanunfari yana taimakawa wajan rage ciwon lokacin al’adar mata hakanan kuma yana maganin Infection.
Kanunfari, musamman manshi yana maganin infection na al’aura ko farjin mata, matsaloli irinsu kaikan gaban mace, zafin gaban mace ko fitar da ruwa.
Ana iya samun man Kanunfari a kasuwa ko kuma ana iya hadashi a gida.
Yanda ake hada man Kanunfari a gida shine, ana samun Kanunfarin a daka a zuba a wata roba ko kwalba, sannan sai a samu man zaitun, kwa-kwa ko wani a zuba a ciki.
Sai a kulle wannan kwalba ko roba zuwa sati daya.
Bayannan sai a samu rariya a tace.
Shikenan an samu man Kanunfari.
Ana iya shafashi a wajan da matsalar take dan samun sauki.
Idan yayi reaction ko kuma matsalar ta ci gaba bayan amfani da man, a tuntubi likita.