
Hukumar ‘yansandan jihar Nasarawa ta musanta cewa an yi garkuwa da wasu dalibai a makarantar Peter’s Foundation Secondary School dake Rukubi Karamar hukumar Doma.
Kakakin ‘yansandan jihar, Ramhan Nansel ta bayyana cewa ta yi magana da shugaban makarantar yace labarin karyane.
Shugaban makarantar yace dalibansa na wasa ne sai suka ga mutane da bindigu, inda suka ruga wajan malaminsu suna cewa ga masu garkuwa da mutane.
Yace malamin ya ce musu su tafi aji, inda acan suka rika gayawa abokan karatunsu cewa masu garkuwa da mutane sun shigo makarantarsu.
Daga nan ne labarin ya yadu, saidai yace maganar gaskiya, mafarauta ne dauke da bindigu ba masu garkuwa da mutane bane.
A wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta, an ga makarantar a kidime inda iyaye suka rika zuwa dan daukar ‘ya’yansu.