
Rahotannin da muke samu na cewa, sojan Najeriya, Muhammad da ya fito ya gayawa Duniya cewa, yana ta so ya ajiye aiki amma na sama dashi sun ki bashi dama, an kamashi an daureshi a Guard Room.
Wani na kusa dashi me sunan Mustapha Muhammad ne ya bayyana hakan inda yace matar sojan ke gaya masa halin da mijinta ke ciki.
Sojan dai ya bayyana cewa wata matsalar iyali ce tasa yake son ajiye aikin nasa inda yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Ministan tsaro da shuwagabannin soji da majalisar tarayya su taimaka masa kan maganar ajiye aikin.
