
Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamnatin tarayya ta kulle makarantun Unity Schools guda 47 saboda matsalar tsaro.

Hakanan daga jihar Filato ma Gwamnatin jihar ta sanar da kulle dukkan marantu sai abinda hali yayi.
A jihar Katsina ma an kulle dukkan makarantun Gwamnati sai abinda hali yayi.
Hakan na zuwane biyo bayan hare-haren ds ake kaiwa babu kakkautawa kan makarantu.
An kai irin wadannan hare-haren akan Makaranta a jihar Kebbi da Jihar Naija.