
Wani barawon Indomie, Usman Abdullahi dan shekaru 24 daga jihar Adamawa ya bayyana cewa ‘yan matansa 3 da ya rabawa Indomie din daya sata babu wadda ta kai masa ziyara gidan gyara hali.
Ya sha Alwashin rabuwa dasu duka da zarar ya fito daga gidan yarin.
Ya bayyanawa mai shari’a wannan labari ne yayin da ake sakw duba shari’ar sa.
A can baya dai an yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari ne.
Saidai a yayin ziyara dan rage yawan mazauna gidan yarin, an sake duba hukuncin da aka masa inda a yanzu aka sashi yin shara.