
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya baiwa Inyamurai baki kan hukuncin daurin rai da rai da akawa Nnamdi Kanu.
Shehu Sani yace ba karshen rayuwa bane.
Yace shi da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo an taba musu daurin rai da rai amma gashi har sun kammala sun samu ‘yanci.
Ya bayyana hakane a shafinsa na X.