
Maryam matar Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ta bayyana fushinta game da ganin Yanda Gfresh da tsohuwar matarsa, Sadiya Haruna ke rugumerungumen juna.
A wata Murya dake ta yawo a kafafen sada zumunta, an ji Maryam na cewa, kotu ce zata rabasu sannan kuma tace zata je ta ajiye masa dansa, Khalid.
Hakanan a wani Bidiyo data wallafa a shafinta na Tiktok an ga Maryam na cewa Allah ya kawo mata dauki.