
Dan bautar kasa, Oyaje Daniel dake aiki a makarantar Judeen International School, Annex Section, Mando dake jihar Kaduna, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, zai Aikata alfasha da ‘yan mata ‘yan makaranta saboda ya gansu da manyan Nonuwa da manyan mazaunai.
Saidai wannan sakon nasa ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda tuni aka daukeshi daga makarantar da yake bautar kasar.
Sannan kuma an tuhumeshi aka kuma mayar dashi ya ci gaba da bautar kasarsa a hedikwatar bautar kasa ta jihar Kaduna.
Saidai Rahotannin sun ce ya nuna nadama sosai kan abinda ya faru kuma ya nemi Afuwa.
An kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan lamarin.
